YADDA ZAKA NEMI SCHOLARSHIP TA WAYAR SALULA
[Fasahar Zamani] Yadda Zaka Nemi Scholarships Ta Wayar Salula Kamar yadda muka sha fada duniya a yanzu anyi cigaba fiye da yadda muke tsammani domin ko yaushe kara zuwa ake da sabbin fasahohi iri-iri. Wato Bahaushe yayi gaskiya da yace “Indaranka Ka Sha Kallo” Yadda Tsarin Yake: Tsarine da zai baiwa dalibi dama ya shigar da bayanansa cewa shine wane dan aji kaza a makaranta kaza a bangare kaza, shikenan cikin ‘yan dakiku zai kawo maka jerin scholarships a wannan yanki namu na Africa abinda ya rage maka kawai sai nema. Tsarin yana lura da yanki da kuma matakin karatun mutum kamar wanda ya gama Sakandire ko mai digiri da mai masters d.s sannan ya baiwa mutum dai-dai dashi a irin salon nan da malam Dan Hausa ke cewa “Dai-dai ruwa dai-dai tsaki”. Yaya Ake Yin Tsarin?: Ka shiga Play Store a wayarka sai kayi searching application mai suna “SomaApp” shikenan kayi installing dinsa a wayarka, kana shigar da bayanan ka, shi kuma Malam SomaApp zai lalubo maka jerin scholarships da...